Tinubu Yayi Alkawarin Karin Albashi Ga Ma’aikata

0 91

Zababben shugaban kasa mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa da ma’aikatan Najeriya cewa za a kara musu mafi karancin albashi da tabbatar da adalchin walwala da tattalin arziki.
Ya bayar da tabbacin yau a Abuja a sakonsa na goyon baya ga ma’aikatan Najeriya dangane da ranar ma’ikata ta duniya ta bana.
Ya kara da cewa a lokacin mulkinsa, ma’aikatan kasarnan za su samu kyakykyawan albashi domin gudanar da rayuwa mai inganci tare da sauke nauyin iyalansu.
Tsohon gwamnan na jihar Lagos ya kuma tabbatarwa da ma’aikatan Najeriya cewa shi mai kare martabar ma’aikata ne kuma yana kan gaba wajen nemo musu hakkinsu.
Yace hakan alkawarine da ya shirya cikawa har a kasan zuciyarsa.
Ya tunatar da ma’aikatan Najeriya cewa muna da cikin fatutuka daya kuma dole mu samu nasara tare.
Yayi nuni da cewa fafutuka ne akan yaki da talauci da jahilci da cututtuka da rashin hadin kai da kiyayyar banbancin addini da kabilanci da dukkan abubuwan dake dakushe zaman lafiya da yalwar arzikin kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: