Dakarun Turkiyya Sun Kashe Wanda Ake Zargin Shugaban Kungiyar IS Ne A Kasar Siriya

0 79

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce dakarun Turkiyya sun kashe wanda ake zargin shugaban kungiyar IS ne a kasar Siriya.

An ce Abu Hussein al-Qurayshi ya karbi ragamar kungiyar ne bayan da aka kashe magabacinsa a shekarar da ta gabata.

Mista Erdogan ya shaidawa kafar yada labarai ta TRT Turk cewa an kashe shugaban IS a wani samame da hukumar leken asirin Turkiyya ta MIT ta kai a jiya.

Ya zuwa yanzu dai kungiyar IS ba ta ce uffan ba game da kisan da akyi ba.

Kamfanin dillancin labarai na reuters ya rawaito majiyoyin Syria suna cewa an kai harin ne a garin Jandaris da ke arewacin kasar, wanda ke kusa da kan iyakar Turkiyya.

Idan zamu iya tunawa dai a watan Nuwamban da ya gabata ne, kungiyar ta sanar da mutuwar shugabanta, Abu al-Hassan al-Hashemi al-Qurayshi. Amurka ta ce an kashe shi ne a wani farmaki da ‘yan tawayen Free Syrian Army suka kai a kudu maso yammacin Siriya a tsakiyar watan Oktoban 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: