Mutum 4.3M Za Su Yi Fama Da Matsananciyar Yunwa A Jihohin Adamawa, Borno Da Yobe

0 89

Shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na samar da abinci ya yi gargaɗin cewa akwai kusan mutum miliyan 4 da dubu 300 za su yi fama da matsananciyar yunwa a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe, dukkansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shirin majalisar yace za’a iya fadawa cikin fargabar ta fari tsakanin watan Yuni zuwa Agustan wannan shekara.

Shirin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar, game da wani rahoto da ya tattara kan matsananciyar yunwa a yankin ƙasashen kudu da hamadar Sahara.

Shirin na WFP ya nuna damuwa kan rikicin da aka kwashe shekaru ana yi da ‘yan bindiga zai iya jefa Najeriya cikin yunwa da tamowa, yayin da miliyoyin mutane suka dogara kan taimako da ake ba su na abinci, wanda kuma suke fuskantar barazanar faɗawa cikin yunwa.

Kimanin mutum dubu 600 na kan gabar faɗawa cikin wannan musifa.

Shirin majalisar yace Mutane za su fuskanci yanayin neman ɗaukin gaggawa saboda ƙarancin abinci, za kuma a fuskanci mummunar matsalar tamowa da mace-mace saboda ƙarancin kai kayan agaji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: