Jihar Jigawa Ta Samu Gudummawar Daruruwan Kayayyakin Yaki Da Cutar Kwalara0

0 68

Kungiyar Action Against Hunger International ta bayar da gudunmawar daruruwan kayayyakin yaki da cutar kwalara ga gwamnatin jihar Jigawa domin daukar matakin gaggawa kan wadanda suka kamu da cutar.

Wannan matakin na daga cikin kokarin da kungiyyar ke yi na hada kai da gwamnatin jihar wajen yaki da barkewar cutar kwalara a jihar.

Da take jawabi yayin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar, jami’ar gudanarwar ayyukan kungiyar masu ba da agaji ta kasa da kasa, Misis Patricia Obrah, ta ce an bayar da tallafin ne a karkashin shirin ‘Emergency Response for People’ da ambaliyar ruwa ta shafa a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ta bayyana cewa, shirin wanda hukumar raya kasashe ta Sweden (SIDA) ta dauki nauyin gudanar da shi, na da nufin magance duk wata bullar cutar kwalara a cikin garuruwan da ambaliyar ruwa ta shafa.

Ko’odinetan wanda ya samu wakilcin jami’in kula da ayyukan, Muhammad Dahiru, ya bayyana cewa jihar Jigawa na daya daga cikin jihohin da ke fama da iftila’in ambaliyar ruwa a ko da yaushe, ya kuma jaddada bukatar hada kai don magance cututtuka. Da yake karbar kayayyakin a madadin gwamnatin jihar, wani jami’in ma’aikatar lafiya Sa’idu Yusuf, ya godewa kungiyar bisa wannan tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: