Gwamnatin Nijeriya ta dawo da dokar kulle domin rage bazuwar corona a kasar gaba daya. Mun samu rahotan cewa daga gobe Talata gwamnatin ta hana zirga zirga daga karfe 12am na dare zuwa karfe 4am na asuba. Kazalika hukumomi sun rufe gidajen kallo. Bayan haka kuma yanzu biki ko wani taro na addini an takaita ta shi kada ya wuce kaso 50 na adadin mutanen da ke zuwansa a baya.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito Mukhtar Mohammed babban jami’ai a kwamitin da Shugaba Buhari ya kafa kan dakile corona na sanar da wadannan sabbin dokoki a wannan Litinin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: