Tsuntsayen daji sun kai biliyan 50 a duniya

0 121

Wani sabon bincike ya nuna cewa adadin tsuntsayen daji a doron duniya ya kai akalla biliyan hamsin, kana suna iya karuwa har zuwa biliyan dari hudu da talatin.

Binciken wanda aka buga a mujallar kimiyya ta duniya na zaman irinsa na farko da aka yi don kimanta yawan tsuntsayen da ake da su.

Ya tattara tarin bayanai daga kwararru da kuma masu bibiyar lamuran tsuntsaye a duniya.

Sakamako ya nuna cewa mafi yawan jinsin da ake samu shi ne na Benu, da yawansu ya kai kusan biliyan daya-da miliyan 600.

Wani abun jan hankalin shi ne adadin yawancin sauran nau’ukan tsuntsaye bai wuce dubu diyar biyar ba.

Masu wannan bincike dai na fatan aikin da suka yi zai taimaka wajen kiyaye bacewar tsuntsayen daga duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: