Gwamnatin Sudan ta Kudu tayi Alkawarin kawo karshen aurar da yara kanana nan da shekarar 2030, kamar yadda Kungiyar Tarayyar Afrika ta bukata na daina Aurar da Yara a Nahiyar.

Manyan Sarakuna 10 na yankin da kuma Jami’an Gwamnati 3 na yankin sune suka, fitar da wannan sanarwa a taron da sukayi domin kawo karshen matsalar a birnin Juba.

Daga cikin abubuwan da taron ya bada shawara, harda irin wanda Jakadan kasar Suwidin Joachim Waern ya bayar na kafa dokar hana aurar da yara.

Kasar Sudan ta Kudu tana daga cikin Kasashe 40 da suke aurar da yara kanana a Duniya, a cewar wani rahoton bincike da aka gudanar a shekarar 2010, inda aka tabbatar da cewa kaso 7 na Matan ana aurar da su ne kasa da shekara 15, inda kuma kaso 40 na Yaran ake aurar dasu kafin shekara 18.

Ma’aikatar Harkokin Matan Sudan ta Kudu ta ce kaso 6.2 kacal na Matan ne suka kammala Firamare, inda ake samun 1 cikin 5 da take kammala Sikandire saboda suna dauke da ciki.

Kazalika, Ma’aikatar ta ce mafiya aka sarin Matan shekarun su baya wuce 15 zuwa 19.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: