Gwamnatin tarayya ta amince da soma amfani da tsarin fasahar 5G a Najeriya

0 96

Gwamnatin tarayya ta amince da soma amfani da tsarin fasahar 5G a Najeriya bayan Majalisar zartarwar ta amince da tsarin.

Ministan Sadarwa ta Kasa da Cigaban Tattalin Arziki ta Fasahar Zamani Dr Isah Ali Ibrahim Pantami shine ya sanar da hakan ga Manema Labarai a fadar Shugaban Kasa, bayan taron majalisar ministoci da aka gudanar ta amince da hakan a jiya Laraba.

Dr Pantami ya ce tsarin 5G na tsawon shekara biyu, ya shafi neman shawarwari da tuntuɓa da gwaji domin tabbatar da ingancinsa.

Ministan ya ce hukumar lafiya ta duniya da kungiyar kamfanonin sadarwa ta duniya sun tabbatar da cewa tsarin ba shi da wata illa ga lafiyar bil adama.

Gwamnatin ta ce tuni ƙasashe da dama na duniya suka soma amfani da fasahar 5G, da suka haɗa da Amurka da Birtaniya da Afirka ta Kudu da kuma Koriya ta Kudu.

Sanarwar ta ce tsarin zai sauƙaƙe amfani da salula musamman ƙarfin intanet da rage yawan cin batir.

Haka kuma, ya ce hukumomin tsaro ne suka bukaci a sauke Layikan Sadarwa a jihar Zamfara domin su sake shirin inganta tsaro a jihar.

Kazalika, ya ce gwamnatin tana kokarin daukan Matakan da suka kamata domin bunkasa tattalin arzikin da kuma samarda tsaro a kasar nan baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: