Gwamnatin tarayya za ta gina filin tashi da saukar jiragen sama a birnin tarayya akan miliyan 500

0 88

Gwamnatin tarayya ta amince da sake wani gini a filin tashi da saukar Jiragen Sama na Kasa da Kasa na Nnamdi Azikiwe dake Birnin Tarayya Abuja akan kudi Naira Miliyan 500.

Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban Kasa, bayan kammala zaman majalisar zartarwa wanda shugaba Buhari ya jagoranta a jiya Laraba.

Haka kuma Garba Shehu, ya ce Majalisar ta amince sabon tsarin jadawalin samar da abinci a kasa.

Malam Garba Shehu, ya ce majalisar ta amince da kasafin hukumomin gwamnati na samar da abinci ga matakan gwamnatoci 3.

Kazalika, ya ce majalisar ta amince da gyaran Madatsar ruwa ta Nassarawa akan kudi Naira Biliyan 1 da Miliyan 200.

Leave a Reply

%d bloggers like this: