Shugaba Buhari ya ce idanuwansa sun gane masa irin ayyukan raya kasar da Gwamnan Jihar Imo yayi

0 60

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce idanuwansa sun gane masa irin ayyukan raya kasar da Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma, ya aiwatar a Jihar.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Jihar Imo, inda ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa wanda gwamnatin Jihar ta aiwatar.

A cewar Shugaba Buhari, gwamnatin Jihar Imo ta aiwatar da ayyukan raya kasa, duk da irin tarin kalubalan da suke addabar jihar.

Haka kuma ya bawa mutanen Jihar tabbacin cewa gwamnatinsa zata cigaba da bin kundin tsarin mulkin kasa.

Shugaba Buhari ya lashi takobin kawo karshen kai hare hare a jihar Imo da ke kudancin Najeriya.

Kazalika ya ce babu wata al’umma da za ta samu cigaba alhalin tana fama da matsalar tsaro.

Shugaba Buhari ya gana da Jagororin Kabilar Igbo a dakin taro na Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: