Cutar Corona ta sake kashe mutane 5 tare da kama mutane 559 a Najeriya

0 71

Cutar Corona ta kashe mutane 5 tare da kama mutane 559 a jiya Laraba a Najeriya.

Cibiyar Dakile yaduwar cututtuka ta Kasa NCDC ita ce ta bayyana hakan a shafin ta na Facebook a ranar Laraba.

Cibiyar NCDC ta ce an samu mutanen da suka harbu da cutar ne a jihohi 14 da suke Najeriya ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

A cewar NCDC mutane 232 ne suka harbu da cutar a Jihar Legas sai Rivers mai mutane 83 da suka harbu da cutar.

Sai Jihohin Enugu – 66, Oyo – 28, Kaduna – 25, FCT – 24, Delta – 22 and Akwa Ibom – 19. 

Sauran Jihohin sune Kwara – 18, Ekiti – 13, Bayelsa – 9, Cross River – 9, Ogun – 6, Kano – 3 and Gombe – 2.

Haka kuma NCDC ta ce an sallami mutane 220 bayan sun warke daga cutar a jiya.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 197,047 ne suka harbu da cutar Corona tun bayan bayyanarta a kasar nan, inda kuma akayi nasarar sallamar mutane dubu 185,379 bayan sun warke.

Kazalika, kimanin mutane dubu 2,578 ne suka mutu a sanadiyar kamuwa da cutar a kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: