Gwamnatin tarayya ta tallafawa Manoma dubu 40,000 da kayan noma wanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Jigawa

0 88

Gwamnatin tarayya ta tallafawa Manoma dubu 40,000 da kayan noma wanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Jigawa.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa SEMA, Alhaji Yusuf Sani Babura, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse.

A cewarsa, an zabi Manoman ne daga Kananan Hukumomi 19 na Jihar nan, wanda kuma suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a shekarar 2020.

Alhaji Babura, ya ce Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, ita ce ta bada gudunmawar kayayyakin.

Haka kuma ya ce Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa ita ce ta dauki nauyin rabon kayayyakin ga mutanen da suka gamu da iftila’in a Kananan hukumomin.

Kazalika, ya ce manufar rabon kayayyakin shine domin a ragewa mutanan da suka gamu da iftal’in radadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: