Majalisar Dinkin Duniya ta ce an garkame ma’aikatanta 16 da ke aiki a birnin Addis Ababa na Kasar Habasha

0 80

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an garkame ma’aikatanta 16 da ke aiki a birnin Addis Ababa na Kasar Habasha.

Mai magana da yawun majalisar Stephane Dujarric ya ce akwai kuma wasu mutane shida da aka saki.

Majalisar ta bukaci ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbata an gaggauta sakin dukkanin mutanen da ake rike da su.

Ko a watan da ya gabata an kori manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya bakwai daga Habasha, bayan zarginsu da katsalandan a harkokin cikin gidan kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu motar agaji da ta isa yankin Tigray tun tsakiyar watan Oktoba.

Hakan kuma na faruwa duk da cewa akwai mutane miliyan bakwai da ke bukatar agajin abinci cikin gaggawa.

Akwai zarge-zargen da ke cewa an kama yan Kabilar Tigrey da dama abinda gwamnati tasha musantawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: