Gwamnatin Tarayya ta ware kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 200 domin gina shafin intanet na Inshora

0 75

Gwamnatin Tarayya a jiya ta bayyana shirin ta na bude shafin kirkirar ayyukan yi ga Matasan da suke zaune a Najeriya dama wanda suke zaune a kasashen waje.

Ministan kwadago da samar da ayyuka na Kasa Sanata Chris Ngige, shine ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar zartarwa.

A cewarsa, Majalisar ta amince da bude shafin mai suna NILEX, wanda zai kasance karkashin Ma’aikatar sa, domin samar da ayyukan yi ga yan kasa.

Ministan ya ce za’a kammala bude shafin cikin Makonni 12 masu zuwa, kuma kwararru ne zasu yi aiki akan sa, ta yadda Matasa masu neman aiki zasu tura bayanan su.

Haka kuma ya ce Majalisar ta amince da zamanantar da Asusun Inshora domin bunkasa tattalin arzikin da kuma saukaka hanyoyin kasuwanci.

Kazalika, ya ce kimanin Naira Biliyan 1 da Miliyan 200 ne Gwamnatin tarayya ta ware domin gina shafin Inshorar ta Internet.

Leave a Reply

%d bloggers like this: