Kotun Burtaniya ta ki bada belin tsohon mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu da matarsa wanda aka kama su da laifin yunkurin cire sassan jikin mutum

0 118

Wata Kotun Majistirin Burtaniya ta ki bada belin tsohon mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu, da Matarsa Beatrice wanda aka kama su da laifin yunkurin cire sassan jikin mutum.

Manema Labarai sun rawaito cewa Yan sanda a Birtaniya sun kama mutane biyu yan Najeriya da zargin shiga kasar da karamin yaro da nufin cire wani sashe na jikinsa.

Bayan gabatar da mutanen a Gaban Kotu, Kotun taki bada Belin su, inda ta umarci a cigaba da tsaresu har zuwa ranar 7 ga watan Yuli.

Cikin wata sanarwa da Yan sandan Birnin Burtaniya suka fitar sun bayyana cewa an gurfanar da mutanen a gaban Kotu ne bayan sashen binciken Manyan Laifuka ya kama su.

Gidan Talabijin na Arise Tv, ya rawaito cewa Masu Gabatar da Kara sun Fadawa Kotu cewa Sanata Ike Ekweremadu, ya kawo wani Yaro dan shekara 15 daga Najeriya, da nufin zai samar masa da abinyi, sai dai kuma bincike ya nuna cewa shi da Matarsa suna son cire wani sashe na Jikin Yaron ne.

Masu Gabatar da kara sun ce Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan, Passport din Yaron ya bayyana cewa shekarar Yaron 21, bayan kuma a Zahiri shekarar sa 15.

Tuni Ma’auratan suka mika Fasfunan su ga Jami’an yan sandan Burtaniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: