Alkalin Alkalan Najeriya Ibrahim Tanko Muhammad ya yi murabus daga mukaminsa

0 85

Majiyoyi a Najeriya sun shaida wa BBC cewa Alkalin Alkalan kasar Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi murabus.

Wani makusancin Alkalin Alkalan ya tabbatar mana cewa babban Mai Shari’ar ya yi murabus ne jiya da daddare.

Murabus din nasa na da alaka da rikicin da ke faruwa tsakaninsa da manyan alkalan kasar 14 wadanda a makon jiya suka zarge shi da rashin iya shugabanci, a cewarsa.

Makusancin Alkalin Alkalan, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya kara da cewa tuni Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya umarci mutumin da ya fi girman mukami a Kotun Kolin kasar ya karbi ragamar tafiyar da ita kafin a nada Alkalin Alkalai na dindindin.

A watan Janairun 2019 ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan kasar bayan dakatar da Alkalin Alkalan wancan lokac, Walter Onnoghen bisa zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

-BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: