Gwamnatin Tarayya tace kawo yanzu ta kashe kudi naira tiriliyan 1 da miliyan dubu 300 a aikin titin Abuja-Kaduna zuwa Zaria-Kano

0 185

Gwamnatin Tarayya tace kawo yanzu ta kashe kudi naira tiriliyan 1 da miliyan dubu 300 a aikin titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano da gadar Kogin Neja ta biyu da kuma babbar hanyar Lagos-Ibadan.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya sanar da haka a yau yayin taron manema labarai na musamman na mako-mako wanda tawagar sadarwar shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

An shirya taron manema labaran domin bashi dama yayi karin haske akan manyan bangarorin da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihoshi ke hada kai wajen aiwatar da wasu manyan sauye-sauyen a ma’aikatar da asasun cigaban gine-gine na shugaban kasa.

Ya lissafa kudade da tsayin manyan titunan da ake ginawa a karkashin asasun cigaban gine-gine na shugaban kasa da suka hada da titi mai tsayin kilomita 375 na Abuja-Kaduna-Zaria-Kano da ya ci naira miliyan dubu 797, sai gadar Kogin Neja ta biyu mai tsayin kilomita 11.59 da ta ci naira miliyan dubu 206, da kuma babbar hanyar Lagos-Ibadan mai tsayin kilomita 127 da ta ci naira miliyan dubu 310.

Leave a Reply

%d bloggers like this: