Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da takwaransa na jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, sun samu kyautar digirin girmamawa a bikin yaye dalibai karo na 25 na Jami’ar Jihar Lagos.

Sauran manyan mutanen da suka samu kyautar digirin digirgir sun hada da shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa da shugabar bankin First Bank, Ibukun Awosika.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Ibiyemi Olatunji Bello, shine ya sanar da haka a lakcar bikin yaye dalibai karo na 25 na jami’ar da aka gudanar yau a Lagos.

Olatunji Bello yace zabarsu daga cikin sunayen mutane dayawa da aka lissafa, bayan dogon nazari da bincike, ‘yar manuniya ce kan gaskiyarsu da sadaukar da kai da kuma gudunmawar da suke bawa kasarsu.

Shugaban jami’ar, Farfesa Bolahan Elias, yace an basu kyaututtukan ne bisa la’akari da kokarinsu da nasarorin da suka samu cikin shekaru a ayyukansu daban-daban.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: