Gwamnatin tarayya tace mutane miliyan 2 ne zasu fara amfana da Naira biliyan 20 daga watan Yuni a wani sabon tsarin da ta kirkira na bada tallafi ga masu karamin karfi

0 51

Gwamnatin tarayya tace kimanin mutane miliyan 2 ne zasu fara amfana da Naira Biliyan 20 daga watan Yunin wannan shekarar a wannan sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta kirkira na bada tallafi ga masu karamin karfi.

Kafin hakan dai angano cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yan kasar nan miliyan 2 ne zasu ke samun naira dubu 5 kowanne wata da kuma wata naira dubu 5 a tsarin bada tallafin  farin kudi ga yan kasar nan da gwamnatin tarayya ta kirkira.

Hakan na nufin gwmanatin zata kashe kimanin naira Biliyan 20 kenan a jimmalace.

A wani rahoto da ma’aikatar jinkai da walwalar al’umma ta fitar a watan Maris na 2022 ta bayyana cewa, gwamnatin ta kara yawan kudaden da yan kasar nan zasu amfani domin dogaro da kansu.

Rahoton yayi nuni da cewa a 2018 jihohi 18 ne aka sanya su a cikin tsarin biyan kudin, sai kuma a 2019 da aka kara yawan jihohin zuwa 24, yanzu kuma aka mayar da adadin zuwa jihohin kasar nan 36 ciki harda Babban birnin tarayya Abuja, wanda ya mayar da adadin masu amfana da tsarin a fadin kasar nan zuwa miliyan 1 da dubu dari 6.

Leave a Reply

%d bloggers like this: