Gwamnatin tarayya tace tana kan bakarta na kawo karshen masu datsen yanar gizo-gizo domin damfara

0 77

Gwamnatin tarayya ta sabunta tsare-tsarenta na kare tattalin arzkin kasarnan na zamani daga masu aikata laifi ta internet, daidai lokacin da take karfafa aminchi tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a kasarnan.

Shugaban hukumar sadarwa ta kasa (NCC), Umar Dambatta, ya sanar da haka a jiya a wajen taron tsaron internet na bana da aka gudanar a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa an shirya taron tare da hadin gwiwar ofishin babban mai bawa shugaban kasa shawara domin manyan masu ruwa da tsaki su tattauna dangane da matsalolin tsaron internet.

Umar Dambatta, wanda ya samu wakilcin kwamishinan hukumar mai kula da masu ruwa da tsaki, Adeleke Adewolu, yace hukumar tana mayar da hankali kan batutuwan da zasu inganta da tsare tattalin arzikin Najeriya na zamani.

A cewarsa, yarda da amana zasu habaka samar da dandalin internet mai inganci, kamar yadda ake samu a manyan kasashen duniya, domin tabbatar da tsaro da amincin adana bayanai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: