Gwamnatin tarayya zata Mikar da hanyar Ka’oji zuwa Birnin Kudu ta nan jihar Jigawa mai Nisan Kilomita 11

0 111

Gwamnatin tarayya zata Mikar da hanyar Ka’oji zuwa Birnin Kudu ta nan jihar Jigawa mai Nisan Kilomita 11 domin magance afkuwar haddura tare da Asarar rayuka a hanyar.

Ministan Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Mista Baba-Tunde Raji Fashola shine ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci hanyar wanda take karamar hukumar Birnin Kudu.

A cewarsa, hukumar Kiyaye Afkuwar Haduru ta Kasa da kuma daidaikun mutane sun damu da irin halin da hanyar take jefa mutane wanda hakan ke jawo asarar rayukan Matafiya.

Ministan wanda babban Sakataren ma’aikatar, Dakta Babangida Hussaini Kazaure ya wakilta, ya ce gwamnatin tarayya zata yi duk mai yiwa wajen ganin ta gyara hanyoyin akan lokaci.

Dr Babangida Hussaini ya kara da cewa ma’aikatar ta tura Injiniyoyi domin duba hanyoyin, tare da mika rahoton ga ma’aikatar akan lokaci.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya zata cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda dokar kasa ta bada damar hakan.

Kazalika, ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa gyara wasu hanyoyin dake kan hanyar domin saukakawa al’umma wajen tafiye-tafiye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: