Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama daya daga cikin Yan fashi da Makamin da suke Addabar hanyar Kano zuwa Maiduguri.

Kakakin rundunar ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse.

A cewarsa a ranar Asabar ne rundunar ta samu bayyanan sirri kan yan fashin, inda sukayi nasarar kama mutum daya daga cikin Jagororin yan fashin wanda yana daga cikin wadanda suka kashe wani Soja mai mukamin Major.

Kakakin ya ce sunyi nasarar kama Haruna Hassan ne a gidansa dake kyauyen Dadin Kowa, a mazabar Dindibis ta karamar hukumar Dutse.

ASP Lawan Shiisu, ya amsa cewa yana daga cikin wadanda suka aiwatar da fashi a babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri.

Haka kuma ya ce mutum ya bayyana cewa yana daga cikin yan fashin da suka kashe wani Soja mai mukamin Major, da kuma raunata mutum 1 a lokacin da suke kan hanyarsu da zuwa Kaduna bayan sun dawo daga jihar Borno.

Kazalika, mutumin ya bayyana cewa yana daga cikin yan fashin da suka tare hanyar Wata Mota kirar Bus a hanyar Kano zuwa Maiduguri, tare da Kwace Kudi Kimanin Naira Miliyan 10 daga hannun Fasinjojin Motar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar nan, ya kara da cewa suna cigaba da bincike domin lalubo sauran yan fashin da suke aiki tare dashi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: