Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wani Yaro dan shekara 17 mai suna Muhammad Muktar Tijjani, bayan ya fada cikin wani Kogi mai suna Semegu a yankin Sobon titi na birnin Kano.

Kakakin hukumar Malam Saminu Abdullahi, shine ya bayyana hakan ga manema labarai cikin wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar bayan yaron ya nutse a cikin Kogin a lokacin da yake wanka.

A cewarsa, sun samu kiran waya ne a ranar Asabar da misalin karfe 2:25 na Rana, daga wani mutum mai suna Muhammad Bello.

Malam Saminu, ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, Ma’aikatan su, sun garzaya wurin da Misalin karfe 2:37, sai dai dauko Yaron a Mace babu rai.

Kazalika, ya ce sun mika gawar Yaron ga Bulaman Kankarofin domin a yi masa Sitira kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: