Gwamnatin tarayyar ta tura tawagar kwararru domin dakile ambaliyar ruwa a jihar Borno

0 88

Gwamnatin tarayyar ta tura tawagar kwararru domin taimakawa wajen dakile illolin ambaliyar ruwa da ta addabi wasu sassan jihar Borno.

Gwamnatin ta kuma sanar da cewa, kwararru za su ci gaba da gudanar da aikin tantance ruwa da gwaje-gwaje tare da gano hanyoyin da ake samu na sinadarai masu hadari, tare da daukar matakan dakile cututtuka masu yaduwa a jihar.

Ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Borno a baya-bayan nan, sakamakon karyewar madatsar ruwa ta Alau, ta haifar da barna da ba a taba ganin irinta ba, inda sama da mutane 30 suka rasa  rayukansu, gidaje 23,000 suka ruguje, sannan mutane 414,000 suka rasa matsugunansu, da muhimman ababen more rayuwa da suka hada da gadoji, hanyoyi, na’urorin lantarki, kiwon lafiya. 

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya Larabar, Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, ya bayyana cewa ya jagoranci manyan jami’an ma’aikatar wajen kai ziyarar jaje a jihar a ranar Juma’ar da ta gabata, domin dakile illolin da ka iya faruwa a sakamakon ambaliyar ruwa.

Ministan ya yabawa Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum bisa gaggawar da ya yi wajen tattara kayan aiki da kuma tabbatar da tsaro da jin dadin al’ummar da abin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: