Uwargidan shugaban kasa ta bayar da gudunmuwar Naira miliyan 500 ga mutanen Maiduguri

0 91

Uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu ta bayar da gudunmuwar Naira miliyan 500 ga mutanen da ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maiduguri, Borno.

Oluremi ta sanar da bayar da tallafin ne a wata ziyarar jaje da ta kai wa Gwamna Babagana Zulum jiya Laraba a Maiduguri.

Uwargidan mataimakin shugaban kasar, Nana Kashim Shettima, ta wakilta, ta mika wa gwamnan naira miliyan 500, tare da yi wa wadanda abin ya shafa addu’a.

Ta yabawa gwamnatin jihar bisa jajircewar da ta yi a dukkan matakai, sannan ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa kungiyar Renewed Hope Initiative, RHI, ga matasa da mata a jihar.

Da yake mayar da martani, Gwamna Babagana Zulum ya yaba da wannan karimcin, inda ya kara da cewa shirin na RHI ya karfafawa mata da dama a jihar gwiwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: