Gwannatin jahar jigwa ta fara aikin rigakafin dabbobi a karamar hukumar Malam Madori

0 646

Karamar hukumar Malam Madori ta fara aiwatar da aikin rigakafin dabbobi na bana, bisa bin umarnin da gwamnatin jihar ta bayar domin kare lafiyar dabbobi a fadin jiha.

Shugaban Sashen Aikin Noma da Albarkatun Daji na karamar hukumar, Malam Abdullahi Zubairu, ya bayyana cewa sun karɓi rigakafi guda 90 daga gwamnatin jiha, inda aka samu nasarar rigakafa dabbobi 8,655 a yankin.

Ya ce za’ayi rigakafin ne ga shanu, raƙuma da sauran manyan dabbobi har guda 100 kowanne, sannan kuma akwai wasu rigakafi da za su yi wa awaki, tumaki da sauran dabbobi ƙanana har guda 3,000.

A nasa jawabin, jami’in rigakafin, Surajo Abdullahi, ya ce sun kuma karɓi rigakafin kaji wanda zasuyi a gonakin kaji da kuma gidajen mutane masu kiwon kaji a gida.

Shugaban karamar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas, ya bayyana cewa za su ci gaba da bin dukkan umarnin da gwamnatin jihar ta bayar domin cika manofofin ta 12, musamman wajen tallafa wa makiyaya.

A karshe, shugabannin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a yankin, Isyaku Ibrahim da Muhammad Jano, sun yaba da yadda karamar hukumar ta samar da isassun magungunan cututtuka domin tallafa wa dabbobin makiyaya.c

Leave a Reply