A ranar Juma’a Fadar Shugaban kasa, ta ce yabon da Buhari zai samu bayan kammala mulkinsa sai ya fi na yanzu.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina,ne ya fadi haka a cikin wata sanarwa mai taken ‘Gwamnatin Buhari a shekara 6.

A wani labarin kuma wasu shuwagabbanin jam’iyyar APC mai mulki, sunce gwamantin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai ci ta samu nasarori da dama cikin shekaru 6 da tayi jagorantar kasar nan fiye da Gwamnatin PDP da kwashe shekaru 16 tana jagorantar kasar nan tindaga 1999 zuwa 2015.

Wannan sanarwar na kunshe cikin wata takarda da sakataren Jam’iyyar APC na kasa  Mr. Lanre Issa-Onilu ya sanyawa hannu, kuma mai magana  da yawun Jamiyyar Salihu Mohammed Lukman ya rabawa manema labarai.

Manyan Jam’iyyar na APC cikin sakuna daban daban da suka wallafi akan wannan ranar, sun bayyana cewa gwamantin shugaba Buhari ta samu nasarori da dama a fanni daban daban.

Kuma kawo yanzu mai magana da yawun Jam’iyyar PDP ta kasa Kola Ologbondiyan bai magantu akan wannan sabon jawabin ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: