Hukumar bunkasa filayen noma ta kasa ta gudanar da taron wayar da kan manoma kan muhimmancin samarda gonakin hukumar a garin Kazaure

0 84

Hukumar bunkasa filayen noma ta kasa NALDA ta gudanar da taron wayar da kan manoma kan muhimmancin samarda gonakin hukumar a garin Kazaure

A jawabinsa wajen taron, jami-in kula da hukumar a jihar Jigawa, Mallam Bello Umar yace jihar Jigawa ta amfana da aiyukan hukumar da suka hadar da gonakin hukumar da rijiyoyin burtsatse da horas da kananan manoma da kuma kaddamar da shirin noman alkama dadai sauransu.

Ya kuma yaba da kokarin masu ruwa da tsaki wajen ganin aiyukan hukumar ya samu nasarar da ake bukata a jihar.

A lokacin taron, Dr Karaye ya gabatar da kasida kan noman alkama tare da gudanar da taron tattaunawa da manoma da matasa da kuma mata.

An samarda hukumar NALDA ne karkashin maaikatar aikin gona da raya karkara ta tarayya da nufin bunkasa filayen noma da kuma tallafawa manoman karkara da nufin bunkasa noman abinchi a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: