Hukumar bunkasa ilmin manya ta jihar Jigawa ta kaddamar da shirin rabon akwatinan radio karkashin shirin ta na koyarwa ta hanyar radio

0 88

Hukumar bunkasa ilmin manya ta jihar Jigawa ta kaddamar da shirin rabon akwatinan radio masu amfani da hasken rana da kayayyakin koyon karatu, karkashin shirin ta na koyarwa ta hanyar radio wanda gwamnatin jiha ta dauki nauyi.

A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a cibiyar koyan karatun manya ta garin Sundumina dake karamar hukumar Birnin Kudu, sakataren zartarwa na hukumar, Dr Abbas Abubakar Abbas yace an bullo da shirin ne domin ilmantar da manya wajen koyan karatu da rubutu da kuma lissafi domin inganta rayuwarsu.

Yace gwamnatin jihar Jigawa ta ware kudi naira miliyan 31 domin gudanar da shirin koyarwar a radio Jigawa na tsawon watanni 6.

Dr Abbas yace cibiyoyin koyan karatun 81 da suke da dalibai dubu 3 zasu amfana da shirin a fadin jihar nan.

Yace cibiyoyin koyan ilmin manya 3 ne zasu amfana da akwatinan radion da kayayyakin koyan karatu a kowacce karamar hukuma dake jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: