‘Yan sanda a jihar Neja sun ce sun dakile harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Jellako da ke karamar hukumar Rafi a jihar

0 62

‘Yan sanda a jihar Neja sun ce sun dakile harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Jellako da ke karamar hukumar Rafi a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana haka jiya a Minna, inda ya ce ‘yan bindiga da dama ne suka tsere da raunukan harbin bindiga, sannan aka sako wasu 15 da aka sace.

Wasiu Abiodun ya ce an kai farmakin ne a ranar 9 ga watan Mayu da misalin karfe 8 da rabi na dare, bisa labarin da aka samu cewa an gano wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne a kusa da kauyen Jellako da ke karamar hukumar Rafi.

Ya kuma tabbatar wa da mazauna garin cewa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan fashi da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Ya ce za a ci gaba da kai hare-hare har sai an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan da ‘yan bindiga suka mamaye.

Ya nemi karin goyon baya daga mazauna wajen ta hanyar bayar da ingantattun bayanai kan hada-hadar mutane da ba a san ko su wanene ba domin daukar matakan tsaro cikin gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: