Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya shiga tsakani tare da sasanta rikicin siyasar da ke tsakanin manyan mutane biyu a siyasar jihar Jigawa wato Sanata Danladi Abdullahi Sankara da Alhaji Isa Muhammed Gerawa.

A karshe taron sulhun da aka gudanar a gidan Gwamnan dake Abuja ya kawo karshen takaddamar siyasar da ke tsakanin manyan mutanen biyu.

Sanata Danladi Abdullahi Sankara ya sake tsayawa takarar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma a karo na uku a tutar jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

Hakazalika, a jihar Kano dake makotaka, hamshakin dan takarar gwamna a jihar, Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya sayi fom na tsayawa takara a jam’iyyar APC domin neman kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a 2023.

A wata sanarwa da ofishin yakin neman zabensa ya fitar jiya, AA Zaura ya yi alkawarin mara baya ga Nasir Yusuf Gawuna, mataimakin gwamnan jihar Kano da dan takarar mataimakin gwamna Murtala Sule Garo.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: