Labarai

Hukumar DSS ta gargadi ‘yan Najeriya akan zargin shirye-shiryen wasu batagari na tashin bama-bamai a manyan gine-ginen gwamnati da guraren taro a lokacin bikin Sallah

Hukumar tsaron farin kaya DSS ta gargadi ‘yan Najeriya akan zargin shirye-shiryen wasu batagari na tashin bama-bamai a manyan gine-ginen gwamnati da guraren taruwar jam’a da wajen hutawa, musamman a lokacin da bayan bukukuwan Sallah.

Hukumar ta DSS ta sanar da gargadin cikin wata sanarwa a yau ta hannun mai magana da yawunta, Peter Afunanya.

Sanarwar tace batagarin na shirin dawo da kasarnan tamkar kafin 2015 lokacin da ake tashin bama-bamai a gurare daban-daban.

Hukumar ta DSS cikin sanarwar ta yi kira ga wadanda suka mallaki wadannan guraren da su yi taka tsantsan tare da aiwatar da muhimman matakan tsaro domin kariya.

Hukumar ta yi kira ga mutane da su gudanar da harkokinsu na yau da kullum tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani bayani mai muhimmanci dangane da ayyukan bata gari.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: