

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci daukacin jam’iyyun siyasar kasarnan da su ajiye batun zabe da bambance-bambancen da ke da alaka da zabe a gefe, su shiga yunkurin gwamnati na dakile matsalar rashin tsaro a kasarnan.
Mai magana da yawun shugaba Buhari, Mista Femi Adesina, a wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, ya ce shugaban kasar ya yi wannan kiran ne a liyafar buda baki da ‘yan kasuwa da shugabannin jam’iyyun siyasa a Abuja.
Hadimin shugaban kasar ya ambato shugaban yana bayyana rashin tsaro a matsayin babbar illar da ke yiwa kasarnan zagon kasa.
Shugaba Buhari ya kara da cewa, a makon da ya gabata ne kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na kasa ya samu gagarumar nasara a taron da ya yi, inda ya bayyana cewa jam’iyyar za ta cigaba da kokarin tabbatar da tsarin dimokuradiyya a dukkanin matakai.
Dangane da saukin gudanar da harkokin kasuwanci a kasarnan, shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi kokari matuka wajen inganta harkokin kasuwanci.