Shugabbin jam’iyyar PDP a jihoshi 19 na Arewa da babban birnin tarayya sun musanta marawa kowane dan takara baya a matsayin wanda jam’iyyar ta amince da shi domin zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Shugabannin sun fadi haka cikin wata takardar bayan taro da aka karanta a karshen taron da suka gudanar a Abuja.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ne ya karantar takardar bayan taron.

Ana rade-radin cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sune kungiyar dattawan Arewa ta lissafa a matsayin ‘yan takarar da ta amince da su daga cikin ‘yan takara hudu na Arewa dake neman takara a jam’iyyar PDP.

‘Yan takarar sune Bukola Saraki, Bala Mohammed, da gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da tsohon manajin darakta na bankin FSB, Mohammed Hayatu-Deen.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: