Hukumar DSS ta tabbatar da gayyatar Abdulaziz Yari

0 237

Hukumar ‘yan sandan farin kaya ta kasa DSS ta tabbatar da gayyatar tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari zuwa ofishinta.
Sai dai hukumar ba ta faɗi dalilin da ya sa ta gayyace shi ba, tana mai musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa an tsare shi ne saboda ya ƙi amsa wayar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Kafin hakan dai a ranar Asabar ne wasu rahotanni da aka wallafa a shafukan intanet suka ce hukumar ta DSS ta kama tsohon gwamnan ne saboda ya ƙi sauraron shugaban ƙasar game da zaɓen shugaban Majalisar Dattawa da aka yi a watan da ya gabata.
DSS ta bayyana labarin a matsayin na ƙarya kuma abin dariya.
Anasa bangaren mai magana da yawun hukumar Dr Peter Afunanya cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin jiya, yace hukumar su zataci gaba da yin ayyukan da ya rataya a wuyanta cikin kwarewa da nagarta.
Ya kuma kara da cewa sun gayyaci Yari domin amsa tambayoyi akan wasu zarge zarge da ake masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: