Hukumar Hana Fasa kwauri ta Kasa ta ce ta kwace kayayyaki 35 tare da motoci 19 cikin watanni 2 da suka gabata a iyakar jihohin Kano da Jigawa

0 81

Hukumar Hana Fasakwafri ta Kasa ta ce ta kwace kayayyaki 35 tare da Motoci 19 cikin watanni 2 da suka gabata a Iyakar Jihohin Kano da Jigawa.

Kwamfuturolan Hukumar na Shiyar B Mustapha Maishanu, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake duba kayayyakin da suka karbo a Kano.

Mista Maishanu ya ce daga cikin kayayyakin da suka karbo sun hada da Buhu dubu 1,265 na Shinkafa, Dila 55 na Gwanjo, da Katan 354 na Taliyar Spaghetti da kuma Buhu 410 na Suga.

Haka kuma ya ce kudin shigo da kayan ya kai Naira Miliyan 76 da dubu 400.

Kazalika, ya ce sun kama mutane 4 bisa zargin su da shigo da kayan sai dai kuma sun bayar da Belin su daga baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: