Labarai

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya ce yan Najeriya a yanzu haka suna kallon Jam’iyar PDP a matsayin mafita daya ga Najeriya

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya ce yan Najeriya a yanzu haka suna kallon Jam’iyar PDP a matsayin Mafita ga kasar.

Da yake jawabi ga Gidan Talabijin na Channels Tv, a jiya, tsohon Gwamnan ya ce shirye-shiryen da Jam’iyar take yi a yanzu domin karbar ragamar Mulki tana yi domin cigaban yan kasa.

A cewarsa, tuntubar da magoya bayan Jam’iyar suke yi a yanzu haka a sassan kasar, zai kara farfado da jam’iyar.

Tuni wasu masu shaa’war tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyar sunyi nisa da fara tuntuba.

Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike, ya gana da masu ruwa da tsaki na Jam’iyar PDP a Jihar Neja, inda ya bayyana cewa babu laifi a yin hakan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: