Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da yan kasar Ukraine miliyan 4 da 900,000 ne suka bar kasar biyo bayan mamayar da Russia ta yi musu

0 70

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da yan Kasar Ukraine Miliyan 4 da dubu 900 ne suka bar Kasar, biyo bayan Mamayar da Russia ta yiwa kasar.

Hukumar Lura da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin yan Ukraine Miliyan 4 dubu 934 da 415 ne suka bar kasar tun bayan da Russia ta yiwa Ukraine mamaya a ranar 24 ga watan Fabreru.

Hukumar ta ce kimanin yan kasashen Afrika dubu 215 ne suka wanda suke karatu da masu aiki a kasar ta Ukraine suka kauracewa kasar inda suka yi sansani a wasu kasashen da suke Makotaka da Ukraine.

Leave a Reply

%d bloggers like this: