Labarai

Fadar shugaban kasa ta zargi limamin coci Matthew Hassan Kukah da kiyyaya ga gwamnatin Buhari tare da amfani da mumbarinsa wajen harkokin siyasa

Fadar shugaban kasa ta zargi babban limamin cocin katolika na Sokoto, Matthew Hassan Kukah, da kiyyaya ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da amfani da mumbarinsa wajen harkokin siyasa.

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, na mayar da martani akan sakon bikin Easter na Matthew Hassan Kukah, wanda a ciki ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da gazawa.

Sawaba ta bayar da labarin sakon bikin Easter na Hassan Kukah inda a ciki ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da lalata Najeriya.

Limamin cocin wanda ya shahara wajen fadin gazawar gwamnatoci, ya kuma zargi shugaban kasa da barin cin hanci da rashawa ya cigaba da yawaita.

A martaninsa, Mallam Garba Shehu yace malamin cocin bai bayar da hujjoji ba dangane da zarge-zargen nasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: