Jami’ar Tarayya dake Dutse ta kammala shirye-shiryen kafa gidan rediyon al’umma na manoma.

Mataimakin shugaban jami’ar, Abdulkarim Sabo Muhammad, shi ne ya sanar da haka jiya a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Mataimakin shugaban jami’ar, wanda yayi magana ta bakin kakakin jami’ar, Abdullahi Yahaya Bello, yace za a kafa tashar a karkashin cibiyar binciken aikin gona ta jami’ar, da nufin ilimantar da manoma.

Ya kara da cewa za a kuma yi amfani da tashar wajen fadakar da al’umma dangane da sauran makamantan matsaloli da nufin karfafa dangantaka tsakanin jami’ar da al’umma.

Ya bayyana cewa jami’ar ta sayo dukkan kayayyakin aikin da ake bukata domin kafa gidan rediyon kuma tana tattaunawa da hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa domin tabbatar da fara aikin gidan rediyon nan ba da dadewa ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: