Hukumar ICPC ta karbo Naira Biliyan 53 daga Bankin Gina Gidaje na Kasa

0 94

Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ICPC ta karbo Naira Biliyan 53 daga Bankin Gina Gidaje na Kasa.

Shugaban Hukumar Mista Bolaji Owasanoye, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da Kwamatin Bincikar Masu Gina Gidaje na Majalisar Wakilai ta Kasa a Abuja.

Mista Owasanoye, ya ce bankin ya karbi kudaden mutanen da sukayi rijista dashi ba tare da gina musu gidajen ba.

Haka kuma ya ce hukumar ICPC zata cigaba da bibiyar bankunan da suke daukar kudaden Jama’a da nufin gina musu gidaje amma basa ginin.

Shugaban Hukumar ya koka kan yadda ake samu karancin gidaje a kasar nan.

Kazalika, ya ce hukumar zata cigaba da yin hadin gwiwa da Kwamatocin Majalisar domin bincikar Badakalar da take fannin Gina Gidaje a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: