Hukumar ilimin kimiyya da fasaha ta jihar Jigawa tace cutar corona bata shafi kokarin dalibanta ba

0 96

Hukumar ilimin kimiyya da fasaha ta jihar Jigawa a jiya, tace, cutar corona kwata kwata bata shafi kokarin dalibanta a 2020 ba.

Babban dakaktan ma’aikatar Alhaji Haladu Ado ne ya bayyana hakan, a lokacin dayake tattaunawa da Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN a birnin Dutse.

Inda ya alakanta kokarin daliban da tsarin nan na koyarwa a Radio da hukumar ta shirya a lokacin.

Kafin hakan dai Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN, ta kawo rahoton yanda gwamnatin jihar Jigawa, ta bullo da tsarin koyarwa ta Radio, domin koyarda da daliban Makarantun firamare dana sakandire, domin yin biyayya ga dokar hana fita da koyarwa a cikin jma’a saboda cutar corona.

Ado ya kara da cewa kaso 68 cikin 100 na daliban da suka zana jarrabawar kasuwanci da kimiyya ta NABTEB na 2020 duk sun samu nasara.

Ya kara da cewa dalibai 1,980 da suka zana jarrabawar kammala sakandire ta NECO, 1,604 sun samu nasara cin manyan darusa 5 ciki harda yaran turanci da lissafi.

Haka kuma cikin wadanda suka zana jarrabawar yammacin afrika ta WAEC 526 cikin 990 da akayi musu rijista, sun samu nasarar cin kwasa kwasai 5 ciki harda yaran turanci dana lissafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: