Gwamnatin tarayya ta kalubalanci matasa da su yi amfani da fasahar kere-kere wajen koyon sabbin sana’o’i

0 121

Gwamnatin tarayya ta kalubalanci matasa da su yi amfani da fasahar kere-kere wajen koyon sabbin sana’o’i, da zama ‘yan kasuwa da kuma samar da sabbin ayyukan yi.

Babban mataimakiya na musamman kan dabarun sadarwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Misis Oge Funlola Modie, ita ce ta bayar da wannan umarni yayin taron horas da matasa da gidauniyar Barista Sam Otoboeze ta gudanar a Abuja.

Ta kuma ce akwai bukatar a tallafawa matasa domin cimma burinsu.

Ta ce horon wata dama ce ta koyo, zama dan kasuwa da samar da sabbin ayyukan yi.

Sam Otoboeze, wanda shi ne ya kafa gidauniyar, ya ce dole ne a yi amfani da matasa miliyan 55 da ba su da aikin yi a Najeriya, domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

An gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gidauniyar Ochima Foundation.

Leave a Reply

%d bloggers like this: