Hukumar ilmi matakin farko ta jihar Jigawa ta raba babura da komfutocin laptop da na’urorin printer ga jami’an kula da ingancin ilmi na sashen ilmi na kananan hukumomi 18

0 68

Hukumar ilmi matakin farko ta jihar Jigawa ta raba babura da komfutocin laptop da na’urorin printer ga jami’an kula da ingancin ilmi na sashen ilmi na kananan hukumomi 18.

A jawabinsa wajen rabon kayayyakin, shugaban hukumar Muhammad Ayuba ya bukaci sakatarorin ilmi na kananan hukumomi da su kara kwazo da himma wajen ziyartar makarantu domin tabbatar da al’amuran koyo da koyarwa a makarantu.

Shugaban wanda ya samu wakilcin wakili a hukumar, Alhaji Nuhu Muhammad Babura, ya kuma shawarci jami’an da su yi cikakken amfani da baburan da kuma naurorin ta hanyar da ta dace.

A jawabinsa, daraktan kula da ingancin ilmi na hukumar, Mallam Hamisu Iliya ya yi fatan jami’an zasu yi amfani da baburan wajen rangadin makarantu domin ganun yadda koyo da koyarwa ke gudanar.

A nata jawabin, babbar sakatariyar ma’aikatar ilmi ta jiha, Hajiya Safiya Muhammad, ta shawarci jami’an da su rinka ziyartar makarantu musamman na karkara domin ganin yadda harkokin karatu ke gudanar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: