Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta gargadi jam’iyyun siyasa cewa za ta rufe shafin ta internet da ake dora sunayen ‘yan takara a zaben 2023 da karfe 6 na yammacin ranar 17 ga watan Yuni domin zabukan kasa da kuma karfe 6 na yamma ranar 15 ga watan Yuli domin zaben jihohi.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wannan gargadin a taron da hukumar ta yi da kwamishinonin zabe, jiya a Abuja.

Mahmood Yakubu ya tunatar da jam’iyyun siyasa cewa an kammala dukkan zaben fidda gwani na jam’iyyu na shekarar 2023 a jiya, yayin da aka fara dora sunayen ‘yan takara a yau.

Mahmood Yakubu ya kara da cewa, domin cimma wannan buri, an horas da jami’ai hudu da dukkanin jam’iyyun siyasa 18 suka zaba, akan yadda za a rika shigar da fom takara a shafin internet da aka samar.

Ya kuma bayyana cewa, an kafa cibiyar tantance sunayen ‘yan takara a hedikwatar hukumar domin karba da kuma gudanar da dukkan ‘yan takara na jam’iyyun siyasa domin zaben 2023.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: