Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani matashi dan shekara 18 bisa zargin kashe wata mata mai shayarwa da danta a wani kauye

Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta kama wani matashi dan shekara 18 bisa zargin kashe wata mata mai shayarwa da danta a kauyen Sabon-Layi da ke karamar hukumar Lamurde a jihar.

Kakakin Rundunar, Suleiman Nguroje, wanda ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar jiya a Yola, babban birnin jihar, ya ce wanda ake zargin da wadanda aka kashen duka mazauna kauyen Sabon Layi ne.

Ya ce wanda ake zargin ya kai wa matar da ya kashe mai suna Talatu Usman hari da yaronta a lokacin da ta je wanka a wani kogi.

Ya ce jami’an ‘yansanda a Lamurde sun kama wanda ake zargin ne a ranar 6 ga watan Yuni.

Kakakin ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Sikiru Akande ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

Da yake nanata kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi, Suleiman Nguroje ya bukaci jama’a da su baiwa ‘yan sanda hadin kai da kuma zama masu bin doka da oda.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: