Hukumar kiyaye aukuwar hadura ta kasa na shirin rage yawaitar hadura akan tituna

0 187

Babban kwamandan hakumar kiyaye aukuwar hadura ta kasa Dauda Biu yace hakumar na shirin rage yawaitar hadura akan tituna, dake sanadin rasa rayuka da raunawa mutane da dama karfin karshen shekarar nan.

Biu ya bayyana haka yayin wani bikin karin girma da aka shiryawa wani jami’i Bisi Kazeem zuwa mukamin DCM wanda aka gudanar jiya a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya bnayar da rahotan cewa Kazeem kafin karin girman ya kasance mai magana da yawun hakumar.

Shugaban hakumar yace hakumar zata gdanar da wani samame a fadin kasa domin tabbatar da lafiyar Ababan hawa a wani yunkuri na magance aukuwar hadura a zirga-zirga. Kazeem da yake mayar da martani bayan karin girman ya jaddada cewa zai rubanya kokarin sa domin tabbatar da ayyukan hakumar bisa doron doka da oda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: