Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) za ta kwace lasisin masu tukin ganganci
Shugaban Hukumar, Corps Marshal Malam Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon gudanar da ayyukan sintiri na musamman na Babbar Sallah da aka gudanar tsakanin ranakun Juma’a 14 ga watan Yuni zuwa Lahadi 23 ga watan Yuni. Ya ce rundunar ta gano abubuwa da dama alokacin sallar fiye da kowane lokaci, don haka akwai bukatar hadin kai da hadin gwiwa a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki. Ya kuma ce rundunar ta yi amfani da wannan, a matsayin wajen samun kayan aiki wanda zai taimaka wajen cimma nasarar da ake bukata.