Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta karbi kujerun aikin hajjin bana 614 daga hukumar aikin hajji ta kasa

0 63

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Jigawa, ta karbi kujerun aikin hajjin bana 614 daga hukumar aikin hajji ta kasa.

Daraktan kudi da mulki na hukumar, Mustafa Umar, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.

Ya ce sun karbi wasikar kujerun da aka warewa jihar Jigawa na aikin Hajjin bana ne daga hukumar kula aikin Hajji ta kasa, inda suke dakon sanar da kudin kujera.

Mustapha Umar, ya ce tuni maniyyata 530 suka bayar da wani abu daga cikin kudin kujerun aikin hajjin da aka soke a bara.

Daraktan wanda shi ne mukaddashin sakataren zartarwar hukumar, ya ce hukumar ta amince da bayar da fifiko ga wadanda suka ajiye wani abu daga cikin kudadensu tun a bara.

Yayi nuni da cewa kujerun aikin hajjin da suka rage za a sayar da su ne ta hanyar wanda ya riga zuwa domin tabbatar da adalci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: