Labarai

Hukumar NDLEA ta bukaci a bai wa jami’an hukumar damar gudanar da gwajin kwayoyi kan ‘yan siyasa masu neman mukamai a Najeriya

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta rubutawa shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, wasika inda ta bukaci a bai wa jami’an hukumar damar gudanar da gwajin kwayoyi kan ‘yan siyasa masu neman mukamai a kasar nan.

Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (Mai Ritaya) ya bayyana haka a yau a Abuja yayin da yake jawabi a wajen bikin karrama jami’an hukumar karo na farko.

Ya kuma ce idan PDP da sauran jam’iyyu za su gudanar da zabukansu na fitar da gwani, hukumar za ta kuma ta rubuta wasiku ga shugabanninsu na kasa tare da neman a bar jami’an NDLEA su gudanar da gwajin kwayoyi ga ‘yan siyasa masu neman manyan mukamai a jam’iyyunsu.

Buba Marwa ya kara da cewa gwajin kwayoyin ya zama tilas domin tabbatar da cewa ’yan siyasa masu rike da mukamai ba su yi amfani da kudaden jama’a ba wajen sayen kwayoyi maimakon samar da ayyukan da ake bukata ga talakawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: